• Thu. May 19th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

TURKIYYA TA KARA MA’AUNIN ISKAR GAS BILIYAN 135 A TEKU

Kasar Turkiyya ta samu nasarar gano ma’aunin iskar gas biliyan 135 ta jirgin ruwa na bincike FATIH.

Shugabab kasar Receb Tayyeb Erdoan ya baiyana labarin da ya nuna yanzu an samu mizanin iskar gas biliyan 540 a yankin Sakarya na bakin teku.

Turkiyya za ta yi amfani da bututu da tsawon sa ya kai kilomita 160 don hada rijiyoyin iskar gas daga yankin Sakarya zuwa babbar cibiyar tara iskar gas din.

Kasar Turkiyya da ke da karancin fetur da gas ta dogara kan shigo da hajar daga Rasha, Azerbijan da Iran. Hakanan ta kan shigo da iskar gas daga Katar, Amurka, Najeriya da Aljeriya.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
4,049 thoughts on “TURKIYYA TA KARA MA’AUNIN ISKAR GAS BILIYAN 135 A TEKU”