• Sun. Jan 16th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

TURJI YA DAU MATAKAN SAKO WASU DA YA DADE DA SACEWA SU 52 A JIHAR ZAMFARA

ByNoblen

Jan 4, 2022 ,

Madugun barayin mutane a tsakanin jihar Zamfara da Sokoto Kachalla Bello Turji ya sako mutum 52 da ya dade da sacewa a jihar Zamfara.
Tuni an tura motocin safa-safa don dauko mutanen da za a shigo da su Shinkafi.
Wannan na iya yiwuwa ya na daga cikin daidaitawa ko yarjejeniya da a ka yi da Turji biyo bayan wasikar da ya aikawa masarautar Shinkafi ya na tayin ajiye makamai don rungumar turbar zaman lafiya.
Turji dai ya addabi yankin Shinkafi a jihar Zamfara da kuma karamar hukumar Sabon Birni da Isah a jihar Sokoto.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *