• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

TUKUR MAMU-A BAR MU MU KAMMALA BINCIKE A TSANAKE DON ZUWA KOTU-DSS

ByNoblen

Sep 13, 2022

Rundunar tsaron farin kaya ta Najeriya DSS ta yi gargadin cewa a daina yi ma ta shishshigi da martani kan kama mawallafin jaridar DESERT HERALD Tukur Mamu yayin ta ke cigaba da gudanar da bincike.

Daraktan hulda da jama’a rundunar Peter Afunanya ya fitar da sanarwar togaciyar kan kama Mamu a Kano bayan dawo da shi daga Masar.

Afunanya ya ce akwai manyan bayanai masu firgitarwa kan binciken da a ke gudanarwa kuma in an kammala za a gurfanar da Mamu gaban kotu.

Jaridar D Herald ta fitar da matsayar nuna rashin amincewa da jagoran ta da nuna tamkar a na kulla ma sa makarkashiya ne biyo bayan kamun.

Hakanan Dr.Ahmad Gumi da ke hulda da Mamu ya zaiyana wadanda su ka kama Mamu da cewa za a iya daukar su a matsayin masu saba doka don bin doka shi ke raba jami’an tsaro da masu aikata laifi.

DSS ta baiyana samun tufafin soja da makudan kudi a ofis da gidan Mamu da ta bincika bayan kamun.

Da alamu DSS ta fata bayanai masu yawa kan Mamu da zai yiwu ta baiyana lokacin gurfanar da shi gaban kotu.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
6 thoughts on “TUKUR MAMU-A BAR MU MU KAMMALA BINCIKE A TSANAKE DON ZUWA KOTU-DSS”

Leave a Reply

Your email address will not be published.