Fadar gwamnatin Najeriya ta nesanta kan ta da tsohon shugaban bankin lamunin gidaje Gimba Yau Kumo wanda hukumar yaki da cin hanci ta jami’an gwamnati ICPC ke tuhuma da hannu wajen badakalar dala miliyan 65.
Mai taimakawa shugaba Buhari kan labaru Garba Shehu ya ce a baya can Gimba Kumo ya taba auren daya daga ‘yan gidan shugaba Buhari, amma tuni auren ya wargaje.
Hakan na nuna fadar ba ta so a rika cewa Gimba Kumo da a ke tuhuma da sace makudan kudin gwamnati na gidane.
Hukumar ICPC ta aiyana Gimba Kumo da wasu mutum biyu a matsayin wadanda ta ke nema ruwa a jallo.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
Very good article! We are linking to this great post on our website. Keep up the great writing.