Tsohon babban hafsan rundunar sojan Najeriya Joshua Dogonyaro ya riga mu gidan gaskiya ya na mai shekaru 80 a Jos.
Marigayin wanda ya yi aiyuka da dama zamanin mulkin soja har da kwamandan rundunar ECOMOG ta Afurka ta yamma.
An kwantar da marigayin a asibitin jami’ar Jos bayan samun shanyewar gefen jiki inda a nan ajali ya same shi.
Dogonyaro na daga cikin manyan sojoji na yankin Lantang a jihar Filato da su ka hada da John Shagaya, Domkat Bali da Jeremiah Husseni da sauran su.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀