• Thu. May 19th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

TSOHON SHUGABAN AMURKA TRUMP YA TAYA NAJERIYA MURNAR DAKATAR DA TWITTER

Tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya tura sakon taya Najeriya murnar dakatar da aikin kamfanin twitter.
Trump wanda twitter ya dakatar da shi gabanin babban zaben Amurka a bara inda ya fadi zaben; ya ce matakin na Najeriya daidai don ta dakatar da twitter don tweeter ta dakatar da shugaban ta.

Trump ya ce twitter da facebook ba su da hurumin dora mutane a kan wata turba mai kyau don ba zai yiwu batacce ya shiryar da mutane ba.

Tsohon shugaban ya ce wannan zai ba da dama ga wasu kamfanonin su baje hajar su don kawo karshen babakeren twitter da facebook.

Donald Trump wanda kazalika facebook ya rufewa shafi na shekara biyu, ya ce da ya so da ya kafa wani dandalin don yanda shugaban facebook Mark Zuckerberg ya yi ta neman magana da shi.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.