Tsohon ministan labarun Najeriya Tony Momoh ya riga mu gidan gaskiya bayan fama da jinya a gidan sa da ke Abuja.
Marigayin wanda ya zama minista zamanin mulkin soja na janar Babangida, ya koma ga Allah ya na mai shekaru 81.
Momoh dan asalin jihar Edo, shi ne shugaban jam’iyyar CPC ta shugaba Buhari da ta narke ta hadu da sauran jam’iyyu su ka kafa APC mai mulki.
Sun yi aiki a APC da injiniya Buba Galadima a matsayin sakataren jam’iyyar.
Momoh ya taba zama editan jaridar Daily Times.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀