• Fri. May 20th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

TSOHON KWAMISHINAN HUKUMAR ALHAZAN NAJERIYA SHEIKH IDOKO YA RIGA MU GIDAN GASKIYA

Allah ya ya yiwa tsohon kwamishina a hukumar alhazan Najeriya NAHCON Sheikh Adam Idoko rasuwa bayan fama da jinya.
Sheikh Idoko wanda ya yi karatu a jami’ar Madina da samun magana da harshen larabci, ya rike matsayin kwamishinan hukumar alhazan mai kula da jihohin kudu maso gabar daga 2007-2014.

Kazalika ya taba rike kujerar babban sakataren hukumar alhazan jihar Enugu. Ya kan gabatar da wa’azi a lokacin aikin hajji da lamuran da su ka shafi aikin hajjin, kuma ya na daga fitattun musulmi ‘yan kabilar Igbo.

Takarda daga jami’ar labarun hukumar alhazan Fatima Sanda ta isar da juyayin hukumar bisa wannan rashi da ya faru a Abuja.
Kazalika Shehunan Islama irin Imam Abdullahi Bala Lau sun nuna juyayi da addu’ar rahama ga marigayin.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.