• Sun. Jan 16th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

TSOHON GWAMNAN OYO ALAO AKALA YA RIGA MU GIDAN GASKIYA

Tsohon gwamnan Oyo a kudu maso yammacin Najeriya Alao Akala ya mutu bayan fama da gajeruwar jinya a garin san a haihuwa Ogbomosho.
Marigayin ya zama gwamnan Oyo ne tsakanin shekara ta 2007-2011.
Abun tunawa game da Akala shi ne, kasancewar sa mataimakin gwamna da ya zama gwamna bayan tsige tsohon gwamnan jihar Rashidi Ladoja.
Marigayi babban dan siyasar Oyo Chief Lamidi Adedibu ne ya mara baya ga Akala bayan Ladoja ya saba tsarin sa na biyaiyar da ta dace.
Har yau ba a samu uban siyasar jiha da kan nada ko canja wanda ya ke so ba kamar maigidan Akala wato Lamidi Adedibu. Mai kamanta irin hakan sai Bola Tinubu a Lagos musamman bisa misalign kawar da tsohon gwamnan Lagos Akinwunmi Ambode ya kawo gwamna mai ci Babatunde Sanwo-Olu.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *