• Wed. May 25th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

TSOHON GWAMNAN ADAMAWA NGILARI YA SAUYA SHEKA DAGA PDP ZUWA APC

ByYusuf Yau

Sep 13, 2020

Tsohon gwamnan jihar Adamawa a Najeriya Bala Ngilari ya sauya sheka daga jam’iyyar sa ta PDP zuwa APC.

Ngilari dai a baya ya samu nasarar kotu wajen tsira daga daurin da a ka yi ma sa daga wata shari’a da hukumar yaki da cin hanci EFCC.

Kamfanin dillancin labarin Najeriya NAN ya ruwaito shugaban APC na Adamawa Ibrahim Bilal ya tabbatar da sauya shekar Ngilari kuma ba da nufin samun wani mukami ba sai don samun damar watayawa a lamuran siyasa.

Adamawa dai ta koma hannun PDP sakamakon zaben 2019 inda Umaru Fintiri na PDP ya yi nasara kan Bindo Jibrilla na APC.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “TSOHON GWAMNAN ADAMAWA NGILARI YA SAUYA SHEKA DAGA PDP ZUWA APC”
  1. Im no longer certain the place you’re getting your information, however great topic. I needs to spend a while learning much more or figuring out more. Thank you for fantastic info I was in search of this information for my mission.

Leave a Reply

Your email address will not be published.