• Fri. May 20th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

TSOHON BABBAN HAFSAN SOJAN AMURKA COLIN POWELL YA MUTU SHEKARA 15 BAYAN RATAYE SADDAM HUSSEIN

ByNoblen

Oct 19, 2021
Tsohon babban hafsan sojan Amurka kuma sakataren harkokin waje bakar fata na farko Janar Colin Powell ya riga mu gidan gaskiya kimanin  shekaru 15 bayan rataye shugaban Iraki Saddam Hussein.
Powell dai shi ya ba da shaidar da ta sa Amurka ta aukawa kasar Iraki da yaki a zamanin tsohon shugaban kasar George W.Bush.
Kazalika tun a zamanin mulkin mahaifin Bush Jr, wato George H.W.Bush a 1991, Powell ya jagoranci kai harin fitar da Iraki daga mamayar kasar Kuwait.
Colin Powell wanda ya yi nadama daga bisani kan shaidar da ya bayar kan Iraki, ya amince an tabka kuskure bisa bayanan da su ka kalawa marigayi shugaba Saddam Hussein laifin tara makaman kare dangi.
Powell ya ce ya ba da shaidar zur da za ta zama sashen bayanan rayuwar sa kuma an tsara karairayin ne daga bayanan wasu a cikin gwamnatin George Walker Bush.
Powell ya riga mu gidan gaskiya ya na mai shekaru 84 sanadiyyar cutar korona bairos.
Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.