• Sun. Jan 16th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

TSARO: YAN BOKO HARAM SUNKAI HARI A GARKIDA

Rahotanni na baiyana harin ‘yan ta’addan Boko Haram a garin Garkida da ke jihar Adamawa a arewa maso gabashin Najeriya.

Bayanai sun nuna ‘yan ta’addan sun zo cikin motoci inda su ka bude wuta da bindigogi da ya sa mutane su ka arce zuwa tsaunukan bayan gari don tsira da ran su.

Irin wannan hari ba wani sabon abu ba ne a wannan yankin don makwabtakar sa da jihar Borno da ke matsayin cibiyar ‘yan Boko Haram.

Ba mu samu wani labari a hukumance na matakai ko martani kan wannan akasin ba.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *