• Sun. Nov 28th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

TSARO: MUTANEN ZAMFARA NA BUKATAR DAGEWA DA KULAWA DA DUKKAN SASSAN JAHAR

ByNasiru Adamu El-hikaya

Sep 26, 2021

Yayin da jami’an tsaro ke cigaba da kai farmaki a dazukan Zamfara don yaki da barayin mutane, wasu mutanen Zamfara na yada sakonni a yanar gizo na bukatar zuba ido kan duka sassan jihar.
Wasu sakonni na nuna har yanzu akwai inda miyagun ke yi wa barazana duk da kafafen sadarwar salula na nan a rufe.
Alamu na nuna yanda a ke daukar yawan barayin ya fi haka don wasu yankunan jihar na cikin fargabar wasu da su ke gani da ba su lamunta da take-taken su ba.
Yayin da mutanen ke yabawa matakan gwamnati na samar da tsaro mai dorewa, masu sakonnin na bukatar gwamnati ta fara tunanin hanyoyin samar da abinci don yanda noma ya shiga halin kakanikayi sanadiyyar wannan yanayi na matakai don kawar da miyagun irin.
Masu bayanan dai da alamu na shiga yankunan jihar Kaduna ne musamman Zaria don samun aiko sakonnin ta yanar gizo.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “TSARO: MUTANEN ZAMFARA NA BUKATAR DAGEWA DA KULAWA DA DUKKAN SASSAN JAHAR”
  1. Just wish to say your article is as astonishing.
    The clearness on your publish is just spectacular and i could think you are knowledgeable in this subject.
    Fine with your permission allow me to take hold of your
    RSS feed to stay updated with forthcoming post.
    Thanks one million and please keep up the rewarding work.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *