• Sat. Jul 2nd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

TSARO: BUHARI YA NADA SABBIN MANYAN HAFSOSHI

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince da murabus din mafi dadaewan manyan hafsoshin soja inda ya nada sabbi don maye gurbin su.

Wannan ya saba da bukatar ‘yan Najeriya da dama har da ‘yan majalisa na neman a sauke su ko a ce an kore su daga mukami.

Maimakon daukar mataki mai tsauri shugaban ya ba su dama su yi murabus ne bayan wuce shekarun su na aikin soja.

Yanzu dai shugaban ya nada Manjo Janar Leo Irabor a matsayin babban hafsan rundunar sojan Najeriya ya maye gurbin Janar Abayomi Olanisakin.

Hakanan ya nada Manjo Janar I Attahiru a matsayin babban hafsan sojan kasa ya maye gurbin Laftanar Janar Tukur Buratai.

Shugaba Buhari ya nada Vice Marshal I.O. Amao ya maye gurbin Air Marshal Saddique Abubakar.

Kazalika shugaban ya nada Rear Admiral A.Z Gambo a matsayin babban hafsan sojan ruwa ya maye gurbin Vice Admiral Ibok Ekwe Ibas.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
2 thoughts on “TSARO: BUHARI YA NADA SABBIN MANYAN HAFSOSHI”

Leave a Reply

Your email address will not be published.