Gwamnan jihar Imo Hope Uzodinma ya ce bai sabawa tsarin mulki musulmi ya dau mataimakin takarar sa musulmi ba.
Hakan na zuwa ne a cigaba da muhawar dacewar tsayawar musulmi a matsayin dan takarar shugaban kasa da daukar mataimaki ma musulmi.
Kai tsaye ma wannan dambarwar ta shafi dan takarar jam’iyyar APC na shugaban kasa Bola Tinubu wanda baya ga fitowa daga kudu da a ke daukar ya dace ya zama kirista, sai ya zama musulmi, don haka ya na bukatar nazari wajen daukar dan takara daga arewa a tsakanin kirista da musulmi.
Uzodinma ya ce ba laifi ba ne takarar musulmi da musulmi don haka ya ragewa jama’a masu zabe su yanke hukunci bisa tsarin dimokradiyya.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀