Kin amincewa da shugaban Amurka Donald Trump ya yi na gudanar da muhawara da dan takarar Dimokrats Joe Biden ta hanyar na’ura ya jefa shakkun gudanar da muhawarar.
Matakin yin taron ta na’ura ya zo ne bayan Trump ya baiyana kamuwa da cutar annoba da hakan ke kawo dari-darin zuwa daf da shi.
Trump wanda tuni a ka sallama daga asibiti ya nuna yanda yake murmurewa daga cutar.
Za a gudanar da babban zaben Amurka ranar 3 ga watan gobe.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀