• Wed. Dec 1st, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

TOH FA! EFCC TA CAFKE TSOHON GWAMNA

Hukumar yaki da cin hanci ta Najeriya EFCC ta yi awun gaba da tsohon gwamnan jihar Abia Theodore Orji.

Hukumar ta kama Orji wanda dan majalisar dattawa ne a filin tashin jiragen sama na Abuja inda ta garzaya da shi ofishin ta da fara tuhumar sa.

An kama Orji da ‘ya’yan sa biyu kakakin majalisar dokokin jihar Abia Chinedu Orji da wani dan na sa Ogbonna Orji.

EFCC na tuhumar mutanen uku da hada baki wajen wawure Naira biliyan 551 a lokacin mulkin Orji daga 2007 zuwa 2015.

A na zargin Orji da badakala da kudin tsaro da a ke ba ba shi Naira miliyan 500 duk wata na tsawon zamanin mulkin sa hakanan da karkatar da kudin aikin gyara muhalli.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *