• Sat. Jul 2nd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

TINUBU YA LASHE ZABEN FIDDA GWANI NA APC DA GAGARUMAR NASARA

Shugaban kwamitin zaben gwamna Atiku Bagudu ya aiyana Ahmed Bola Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwanin na APC da kuri’a 2,271.
Sunan Tinubu a ke ta ambata tun fara kidayar kuri’a kafin can a ambaci wanda ya zo na biyu Rotimi Amaechi mai kuri’a 316 sai mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo mai kuri’a 235.
Abun mamaki Rochas Okorocha da Pastor Tunde Bakare ba su samu ko kuri’a daya ba.
Daraktan ofishin kamfen din mara baya ga Tinubu, Aminu Sulaiman ya ce sun kasa sun samu nasarar bazata.
Ga mataimakin shugaba Yemi Osinbajo da magoya bayan Tinubu ke ganin ya juya mu su baya kasancear sa dan gidan Tinubu ne, Aminu Sulaiman ya ce santsin takalmi ne ya kwaashe shi.
Msgoya baya na ta murna da shiga yanayin buki.
Shugaba Buhari ya gargadi ‘yan jam’iyyar da kar su sake PDP ta dawo a zaben 2023 don ya ce za su mayar da hannun agogo baya kan abun da ya zaiyana da nssarorin da gwamnatin sa ta cimma.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
2 thoughts on “TINUBU YA LASHE ZABEN FIDDA GWANI NA APC DA GAGARUMAR NASARA”

Leave a Reply

Your email address will not be published.