• Tue. Nov 30th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

SOYAYYA: TAYAYYA ZAN SACE ZUCIYAR MACE

Tayayya zan sace Zuciyar Mace?

A gaskiya sace zucciyar mace abu ne mai sauki ga wanda ya gane sannan kuma abu ne mai wuya ga wanda bai gane ba. Tabbas idan dai har kana so ka yiwa mace satar zucciya dolene sai ka bi dokoki kamar haka:

1. # Jan_Aji: ka sani fa mace bazata iya mallaka maka kanta hakannan kawai ba dolene sai ta ja maka aji dan ta gane halayenka da haƙurinka sannan kuma zata so ta gane ko da gaske ne kake sonta ko ba da gaske ba sabida mata sun tsani duk wani saurayin dake shirin yaudaransu, idan har kaga ka zowa mace kai tsaye ta amince dakai ba tareda jan class ba, to fa ka tsoraci lamarinta domin mace idan har cikakkiyar gogaggiyar mace ce to zata ja maka class sosai har sai ka kusan yin kuka tukunna.

2. # Hakuri: Tabbas dolene sai ka zamo mai hakuri idan ba haka ba bazaka samu damar lashe jarabawar da mace zata yima ba sabida zakaga ababe da dama masu gasa zucciya, idan har baka zamo mai hakuri ba; to kai da yin soyayya da mace saidai a slow…

3. # Gaskiya: mace tafi son saurayin da ke gaya mata gaskiya kai tsaye, idan har kai makaryaci ne to ina mai tabbatarma da cewa idan har tazo ta gane sirrinka zaka sha kashi, dan haka ake kwatanta gaskiya daidai gwargwado.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *