• Sun. Jan 16th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

TASHOSHIN DAKATAWAR MANYAN MOTOCI DON HUTAWA SUN FARA AIKI A NAJERIYA

Tashoshin dakatarwar manyan motoci da sauran motoci safa kan manyan titunan Najeriya sun fara aiki don rage yawan hatsari da ke faruwa a sanadiyyar gajiya da direbobi ke samu.

Hukumar hada-hadar kasuwanci ta jiragen ruwa “shippers council” ta samar da tsarin da hadin guiwar gwamnatoci da ‘yan kasuwa.

Wadanan tasoshin dai da za su taimaka wajen rage cunkushen gefen hanya a wasu garuruwa da manyan motoci ko cin zango kafin tafiya irin su Kari a jihar Bauchi, Marabar Jos, Tafa, Gwalam, Isia Langwa da sauran su, tsari ne da kasashen duniya musamman masu cigaba su ka dauka don kare rayuka da dukiya.

A taro da masu ruwa da tsaki na hanya a Abuja, babban sakataren hukumar kula da hada-hadar kasuwanci ta jiragen ruwa Mallam Hassan Bello ya nanata yanda taswirar tashoshin za ta kasance da zai zama har da bunkasa tattalin arziki.

Shugaban sashen kula da hadin guiwa da sassa masu zaman kan su don kafa tasoshin, Mustapha Zubairu ya ce tuni wasu daga tashoshin sun fara aiki.

Manyan motoci dai har yanzu su ne babbar hanyar hada-hadar kayan masarufi a Najeriya don rashin hade birane da layin dogo, da hakan ke sa motocin masu nauyi murkushe tituna da haifar da ramuka da jan jawo mummunan hatsari.

Hakanan hatta kafa tashoshin sauke hajar teku a kan tudu ko yankunan da ba sa gabar teku na arewa na samun cikas don rashin ingancin layin dogo, don haka sai manyan motoci da a ke kira DOGUWA ke kwana tafiya don kai muhimman kayaiyakin.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *