• Mon. Jan 17th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

TASHIN LITAR FETUR-KUNGIYAR ‘YAN KWADAGON NAJERIYA NLC NA SHIRIN ZANGA-ZANGA

ByNoblen

Dec 29, 2021

Kungiyar ‘yan kwadagon Najeriya NLC na shirin gudanar da zanga-zanga don nuna rashin amincewa da shirin kara farashin litar fetur.
A wasika ga shugabannin kwadago na jihohi daga helkwatar kungiyar a Abuja, NLC ta bukaci duk rassan ta su fara shirin zanga-zangar a ranar 27 ga watan fabreru 2022.
Yayin zanga-zangar da za ta hada da kungiyoyin fararen hula, za a mika wasika ga gwamnonin jihohi kan manufar.
A 2016 dai kungiyar kwadagon ta gamu da bijirewar jama’a yayin da ta kira yajin aiki da zanga-zanga lokacin da gwamnatin Buhari ta tada farashin litar daga Naira 87 zuwa 145.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “TASHIN LITAR FETUR-KUNGIYAR ‘YAN KWADAGON NAJERIYA NLC NA SHIRIN ZANGA-ZANGA”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *