• Sat. May 21st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

TASHIN DALA-KAYAN MASARUFI A NAJERIYA NA KARA TSADA

Tuni tashin farashin dala kan naira ya haddasa tsadar muhimman kayan masarufi da mutane su ka fi bukata a Najeriya.

Cikin abubuwan da su ka kara kudi har da sinadaran dafa abinci da buredi.

Wasu matakan bankin Najeriya da zummar samun wadatacciyar dala su ka sanya kara faduwar darajar naira.

Abun da ke ba da takaici shi ne karawa wasu kayan da ba sa alaka da dala farashi don cin gajiyar bulus a sanadiyyar raguwar darajar kudin Najeriya.

Dala daya dai yanzu a kasuwar canji ta doshi naira 500 kuma maimakon lamarin ya rika gyaruwa sai farashin ke kara dagawa.

Dogaro ga odar kaya daga ketare don rashin kera su a Najeriya dama shigo da tataccen man fetur daga kasashen waje na daga dalilan da kudin Najeriya ke samun koma baya in an kwatanta da dala, fam din Ingila, Euro ta turai da sauran su.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “TASHIN DALA-KAYAN MASARUFI A NAJERIYA NA KARA TSADA”

Leave a Reply

Your email address will not be published.