• Sun. Dec 5th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

TARON MDD-SHUGABA BUHARI YA BARO NEWYORK YA NUFO ABUJA

ByHassan Goma

Sep 26, 2021

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya baro birnin New York din Amurka inda ya nufo babban birnin Najeriya Abuja.
Shugaban wanda ya halarci taro na 76 na babban zauren majalisar dinkin duniya ya cika kwana 7 cif da tun farko fadar Aso Rock ta sanar zai yi a tafiyar.
Muhimman abubuwan da shugaban ya baiyana a jawabin sa gaban zauren akwai neman yafewa kasashe masu tasowa jibgin bashin da a ke bin su da kan sa amfani da ‘yan kudin raya kasa wajen biyan bashin kasashe masu arziki a duniya.
Hakanan shugaban ya bukaci a hada kai wajen yaki da dabi’ar karbar mulkin shugaba da ya faru a wasu kasashen Afurka.
Shugaban ya samu ganawa ta musamman da babban sakataren majalisar dinkin duniya Antonio Guterres.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *