‘Yan Taliban da su ka karbe ragamar mulkin Afghanistan, sun nuna murna yayin da rukunin karshe na sojan Amurka ya fice daga kasar.
Jiragen karshe da kaya sun tashi daga filin jirgin saman Kabul da hakan ke nuna kammala jigilar jama’ar Amurka daga kasar ta Afghanistan.
‘Yan Taliban sun tsaya su na kallo har jiragen su ka bace a sararin samaniya inda daga nana su ka harba bindigar nuna murnar rabuwa da mamayar Amurka ta shekaru 20.
A Washingtom babban Kwamandan rundunar sojan kasar Janar Frank McKenzle ya aiyana kammala dogon yakin na Amurka a Afghanistan.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
If you are going for best contents like me, simply
go to see this web page everyday as it offers feature contents,
thanks