• Fri. Jul 1st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

TALIBAN KA IYA DADEWA KAN MULKI IN TA TSAYA KAN ADALCI-DUKAWA

TALIBAN KA IYA DADEWA KAN MULKI IN TA TSAYA KAN ADALCI-DUKAWA

Duk da yanda sabuwar gwamnatin Taliban a Afghanistan ta ba da mamaki don ba da mukamai ga tsoffin shugabannin kungiyar, yanda gwamnatin za ta gamsar da al’umma cewa za ta yi mulkin bisa adalci da yi wa wasu ‘yan kasar da ba sa danyen ganye da kungiyar uzuri ya zama abun sharhi.

A yanzu dai akalla Taliban ta murkushe duk wata turjiya daga masu adawa da ita, inda yanzu kalubalen inganta tattalin arzikin kasar da sake gina kasa ne ya zama babbar ajandar gwamnatin.

Masanin kimiyyar siyasa na jami’ar Bayero ta Kano Dr.Sa’idu Ahmed Dukawa ya ce sauya salo da tabbatar da adalci ne zai sa gwamnatin Taliban ta yi dogon zamani kan mulki.

Dr.Dukawa ya ce ya zama mai minimmanci Taliban ta bar mata su yi karatu da yin aiki inda ya dace da su don hakan bai sabawa shari’ar Islama ba.

Masanin ya jaddada cewa ta hanyar bin dokokin musulunci da kaucewa wuce gona da iri Taliban za ta yi dogon zamani bisa karagar madafun ikon birnin Kabul

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.