• Fri. May 20th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

TABARBAREWAR TSARO A NAJERIYA TA ZAMA BABBAR JARRABAWA GA KOWA A NAJERIYA-BAFARAWA

Tsohon gwamnan jihar Sokoto Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa ya nuna matukar damuwa kan tabarbarewar tsaro a Najeriya, ya na mai cewa kalubalen ya wuce matsayin a tsaya a na dorawa gwamnati laifi don sai kowa ya yi tsayin daka kafin a samu saukin da a ke bukata.

Alhaji Bafarawa wanda ke zantawa da Bashir Ibrahim Idris na rediyon Faransa, ya ce sai da kasa kowa zai iya tabuka wani abu, don in ba kasar ba amfanin duk wata kujerar mulki.

Yayin da ya ke nuna takaicin yanda barayi da ‘yan bindiga kan samu kyaliyar talakawa wajen huldar cinikayya kamar kai fetur ko katin waya, ya ce kowa na da na sa laifi da sai an taru gaba daya an yi gyara don samun maslaha.

Dan jaridar ya nemi jin ko Bafarawa na kare gwamnati ne?, a nan bayanan na Bafarawa na nuna an wuce matsatin zargin wani ko masu mukami, kowa sai ya kula ya ba da tasa gudunmawar don ceto musamman yankin arewacin Najeriya da illar ta ta’azzara.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.