• Sun. Dec 5th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

TA TABBATA TSOHON GWAMNAN BANKIN NAJERIYA BA ZAI SAMU TIKITIN TAKARAR GWAMNAN ANAMBRA BA

Jerin sunayen da hukumar zaben Najeriya INEC ta fitar don zaben gwamnan jihar Anambra ya kasance ba sunan tsohon gwamnan babban bankin Najeriya CBN Charles Soludo a inuwar jam’iyyar APGA.

Ita dai AFGA na da tagomashin lashe zabe a jihar don kasancewar ta asali daga uban ‘yan awaren Biyafara marigayi Odumegwu Ojukwu ne.

Sunan Chuma Umeji ne ya fito a matsayin dan takarar da wata malamar jami’a Lilian Orogbu a matsayin mataimakiya.

Hakanan jam’iyyar PDP ta fito ba dan takara a zaben da za a gudanar a watan nuwamba.
Gwamnan jihar Willie Obiano na AFGA zai kammala wa’adin sa na biyu kuma a karshe a karshen shekarar bana.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *