• Fri. Jul 1st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

TA TABBATA IDIN KARAMAR SALLAH ALHAMIS DIN NAN A NAJERIYA DA SAUDIYYA

Biyo bayan rashin ganin watan Shawwal a talatar nan yayin da azumin Ramadan ya cika kwana 29, ya nuna za a gudanar da idin karamar sallah ranar alhamis 13 ga watan nan na Mayu.

Sanarwa daga fadar mai alfarma sultan Muhammad Sa’ad Abubakar ta ce ba a ga wata ba daga dukkan sassa don haka alhamis din ne za ta zama 1 ga watan shawwal na hijra 1442.

Rahotanni daga Saudiyya ma na baiyana ba a ga watan ba don haka za a gudanar da idin a alhamis din da yardar Allah.

A ka’idar kalandar hijira wata na yin kwana 29 ko 30 don haka ba ma bukatar sai an duba wata a larabar nan 12 ga watan nan na Mayu.

Tuni gwamnatin Najeriya ta aiyana laraba da alhamis din nan hutu don wannan lokaci na idin karamar sallah.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “TA TABBATA IDIN KARAMAR SALLAH ALHAMIS DIN NAN A NAJERIYA DA SAUDIYYA”
  1. For most recent news you have to go to see world wide web
    and on the web I found this website as a best website
    for most up-to-date updates.

Leave a Reply

Your email address will not be published.