• Mon. Jan 17th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

TA HANYAR FIDDA ZAKKAH, ZA A IYA GINA AL’UMMA TA ZANA TA KWARAI-SHEIKH BALA LAU

Shugaban JIBWIS Sheikh Abdullahi Bala Lau ya ce ta hanyar fitar da zakkah yanda ya dace za a samu nasarar gina al’umma ta zama ta hau hanyar gaskiya da amana.
Shehun malamin na wa’azi ne ko gabatar da nasiha a Hadeja Jihar Jigawa albarkacin wani aure da ya shafi gidan tsohon babban shugaban hukumar shige da fice Muhammad Babandede.
Sheikh Bala Lau ya kawo kisser wani mai dukiya da ya ba da zakkah a asirce ga mutum 3 inda daga baya ta baiyana ma sa na farko barawo ne, na biyu karuwa ce na uku kuma wani mai kudi ne gafalelle.
Mai dukiyar nan ya shiga damuwa cewa ya yi bakin kokari ya raba zakkah ga mutanen kirki amma bai samu nasarar isar da sakon ga hannu mai kyau ba.
Bawan Allan ya kwanta ya yi mafarki cewa Allah ya karbi aikin sa don duk mutanen 3 a sanadiyyar zakkar sun koma mutanen kirki.
Cikin wadanda su ka gabsatar da nasiha, da Sheikh Kabiru Haruna Gombe wanda ya ja hankalin malamai masu rawar kai da cewa sun fi kowa sanin komai, su ji tsoron da yin aiki don Allah ta hanyar mutunta sauran malamai.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *