• Sat. Nov 27th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

SUDAN ZA TA MIKA TSOHON SHUGABA ELBASHIR GA KOTUN DUNIYA

ByNoblen

Aug 12, 2021 ,

Kasar Sudan ta yanke shawarar mika tsohon shugaban kasar Omar Hassan Elbashir ga kotun duniya don fuskantar shari’ar zargin sabadiyyar mutuwar mutum dubu 300 a yankin Darfur.

Ministar wajen Sudan Mariam Almahdi ta baiyana sabon matsayin na gwamnatin rikwan ta Sudan.

Wannan ya biyo bayan ziyarar da mai shigar da shari’a na kotun Karim Khan birnin Khartoum.

Za a mika Elbashir da a ka yi wa juyin mulki a 2019 da sauran mukarraban sa ga kotun ta duniya.

Da alamu sabbin hukumomin birnin Khartoum na neman karin kusaci ne ga sauran kasashen duniya musamman na yammacin duniya da ke daukar Elbashir a matsayin babban mai laifi ko abokin gaba.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *