• Mon. Jan 17th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

SUDAN-AN HARBE ‘YAN ZANGA-ZANGAR KIN JININ GWAMNATIN SOJA 4

ByNoblen

Dec 31, 2021 ,

Rahotanni daga Sudan na baiyana cewa an harbe masu zanga-zangar kin jinin mulkin soja a kasar kasar Janar Abdelfatah Burhan su 4.
Jami’an tsaro sun yi kisan ne a birnin Oumdurman da tasirin sa tamkar babban birnin kasar ne Khartoum.
Masu zanga-zangar sun share kwana na 11 a gagarumin gangami a babban birnin kasar Khartoum tun kwace mulki da soja su ka yi a ranar 25 ga watan oktoba.
Dubban mutane kan fito don zanga-zangar duk da takaitawa ko birkita hanyoyin sadarwar yanar gizo da a ka yi.
Zuwa yanzu dai majiyoyin likitoci na nuna mutum 52 ne su ka mutu a sanadiyyar zanga-zangar.
Duk da dawo da firaminista Abdullah Hamdok kan mukamin sa, bai sa masu zanga-zangar barin kan tituna ko yada kwallon mangoro ba.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *