• Mon. Jan 17th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

SOJOJIN TARON DANGI SUN HARBO JIRAGE MARAR SA MATUKA BIYU DA A KA TURA FILIN JIRGIN BAGADAZA

Sojojin taron dangi da Amurka ke marawa baya a Iraki sun harbor jirage marar sa matuka biyu da a ka tura filin saukar jiragen sama na Bagadaza a kasar Iraki.
Harin dai ya zo a daidai ranar tunawa da kashe babban janar na Iran Qassim Soleimani da Amurka ta yi a filin jirgin.
A jikin daya da fukafukan jirgin marar matuki an rubuta daukar fansa ga Soleimani.
An auna jiragen biyu ne kan cibiyar soja ta Amurka da ke filin jirgin wacce ke kunshe da masu ba da shawara.
Ba labarin jiragen sun yi wa filin na farar hula illa ko taba lafiyar jami’ai.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *