• Wed. May 25th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

SOJOJIN RASHA NA NAUSAWA ZUWA BABBAN BIRNIN UKRAINE WATO KYIV

Sojojin Rasha na kara nausawa don kwace babban birnin kasar Ukraine wato Kyiv inda tuni a ka ba da rahoton dirar wani makami mai linzami na Rasha da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 10 a birni na biyu mafi girma a Ukraine, Kharkiv.
Hotunan tauraron dan-adam na nuna dogon layin motocin sojan Rasha a tsawon mil 40 na tafiya don gama aikin mamaye Ukraine.
Rasha na nanata cewa ba ta auna fararen hula kuma ba son kwace Ukraine ta ke son yi ba, amma ta na son kwance damarar yaki ne na Ukraine da ke zama kawar kasashen yammacin turai.
Tuni wannan mamaya ta haddasa arcewar mutum dubu 870 daga Ukraine mai yawan mutum miliyan 44.
Duk da maganganun caccaka da shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ke furtawa na nuna Rasha na son murkushe tarihin Ukraine ne, hakan bai hana bukatar a tsagaita wuta da hawa teburin shawara ba.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
50 thoughts on “SOJOJIN RASHA NA NAUSAWA ZUWA BABBAN BIRNIN UKRAINE WATO KYIV”

Leave a Reply

Your email address will not be published.