Ministan gwamnatin Yaman ta Abed Rabbo ya ce rundunar Quds ta Iran ke shugabancin yankunan da ‘yan tawayen houthi ke rike da su a kasar da ke cikin fitinar ‘yan tawaye.
Ministan labarun Yaman Muhammad Al-Eryani ya baiyana cewa kwamandan Quds Hassan Erlo ne asalin shugaban yankunan da houthi ta ke rike da su ciki har da asalin babban birnin kasar Sanaa.
Matsayar gwamnatin Yaman ita ce houthi na karbar umurni ne kai tsaye daga birnin Tehran da ke samar da makamai da dabarun yaki ga kungiyar ta tawaye.
Eryani ya ce wannan ya nuna muradin Iran na fadada tasirin ta, ta hanyar mallake Yaman da kuma neman yin hakan ga sauran yankin na Larabawa.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀