• Mon. May 23rd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

SOJOJIN NAJERIYA SUN BINDIGE ‘YAN AWAREN BIYAFARA 4

Sojojin Najeriya sun dau matakin bindige ‘yan awaren Biyafara 4 a yankin Ihiala da ke jihar Anambra, a yayin da ‘yan bindigar ke neman tilasta hana mutane fita.
Biyo bayan kira ta waya daga mutane kan illar ‘yan awaren, sojojin sun garzzayo su ka tarar ‘yan bindigar na harbe-harbe, don haka su ka dau matakin gamawa da su.
Kakakin rundunar sojan Najeriya Onyeama Nwachukwu ya baiyana labarin, sai dai sanarwar ba ta baiyana ainihin lokacin da matakin ya auku ba.
Sanarwar ta kara da baiyana juyayin rasa ran jami’an ta biyu a arangamar da kuma samun raunin wasu biyu biyo bayan lalacewar motar da ta ke dauke da su

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.