• Tue. Nov 30th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

SOJOJIN LEBANON NA BUKATAR TAIMAKON KETARE DON KARANCIN KUDI

ByNoblen

Jun 18, 2021 , ,

Sojojin kasar Lebanon da ke fama da kuncin tattalin arziki sun mika kokon bara ketare don neman tallafi.

Kiran ya zo ne a taro ta na’ura na kungiyoyin tallafawa Lebanon 20, kasashen Larabawa, majalisar dinkin duniya da kungiyar taraiyar turai.

Shugaban sojojin Lebanon Janar Joseph Aoun ya yi kokarin rufa lamarin da nuna duk da kalubalen, amma sojojin na da kuzari kuma su na nan a shirye don kare kasar.

Faransa da hadin guiwar Italiya da majalisar dinkin duniya na yunkurin nemawa sojojin Lebanon tallafin abinci, magani da kayan aiki don yanda faduwar darajar kudin kasar ya kawo durkushewar karsashin rundunar.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *