• Sun. Jan 16th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

SOJOJIN ISRAILA SUN HARBE BAPALASDINE AMIR ATEP YAYIN DA YA NUFO WASU ISRALAWA DA WUKA

ByNoblen

Jan 1, 2022 ,

Sojojin Israila sun harbe wani Bapalasdine yayin da ya fito daga motar a magamar hanya rike da wuka ya nufo inda wasu sojojin Israila ke jiran mota a gabar yammacin kogin Jodan.
Bapalasdinen mai suna Amir Atep Reyan da alamu ya na son yin kisan gilla ne da wukar, inda kafin isa bigiren sojoji su ka harbe shi.
Daga bisani ma’aikatar lafiya ta Israila ta tabbatar da mutuwar Reyan daga raunukan harbi da ya samu.
Kalubalen na faruwa ne a lokacin da Palasinawa da Yahudawa su ka mamayewa garuruwa kan yi amfani da wuka don kai hare-haren ga Yahudawan.
A duk irin wannan hari, sojoji da ‘yan sandan Israila kan bude wuta su kashe wanda su ke gani ya na barazana ga tsaron lafiyar su.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *