• Sat. May 21st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

SOJOJI UKU SUN RASA RAN SU A FADA DA ‘YAN BINDIGA A NEJA-GWAMNA BELLO

Gwamnan jihar Neja Abubakar Sani Bello ya ce sojoji uku sun rasa ran su a fafatawa da ‘yan bindiga a yankin Magama da ke jihar.

Sani Bello wanda ya ke magana da manema labaru bayan taron tsaro a Minna fadar jihar, ya ce sojojin sun samu nasarar hallaka wasu daga ‘yan bindigar.

A halin yanzu an gano gawa biyu yayin da a ke bin sawun ‘yan bindigar da zummar karya alkadarin su.

Gwamnan ya ce an samu wata nasarar ta komawar wasu daga ‘yan gudun hijira yankunan su na asali kamar a karamar Shiroro, Munya da Mariga.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.