• Wed. May 25th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

SOJOJI SUN KIFAR DA GWAMNATIN BURKINAFASO

Sojoji sun kifar da gwamnatin kasar Burkinafaso da ke yankin Afurka ta yamma inda nan take su ka dakatar da aiki da tsarin mulki da rufe kan iyakar kasar.
Sojojin a sanar da juyin mulkin a sako ta gidan talabijin da ke nuna kawar da shugaba Rock Kabore daga kan mulki da korar majalisar dokokin kasar.
Laftanar Kanar din soja Paul Henry Sandaogo Damiba ya sanya hannu kan takardar sanarwar juyin mulkin, inda wani sojan Sidsore Kader Ouedraogo ya karanta ta a gidan talabijin.
Sojojin sun ce duk wadanda a ka kama an adana su a wajen mai tsaro.
Masu juyin mulkin sun ce sun gudanar da matakin ne don yanda shugaba Kabore ya gaza samar da tsaro da hada kan al’ummar Burkinafaso.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.