• Wed. Dec 1st, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

SOJOJI SUN CETO KARIN DALIBAN KOLEJIN GWAMNATI TA YAWURI

Dakarun sojan Najeriya sun baiyana sake samun nasarar ceto karin daliban kolejin gwamnatin taraiya ta Yawuri da barayi su ka sace.

Kakakin rundunar sojan Najeriya Onyeama Nwachukwu ya baiyana labarin a wata sanarwa.

Nasarar ta hada da ceto malami daya da dalibai uku.

Tun farko rundunar ta yi nasarar ceto dalibai biyar da malamai biyu.

Yanzu haka soja na cigaba da yunkurin ceto dukkan daliban a dajin da barayin ke tsare su.

In za a tuna sojan sun murkushe gomman barayin a dajin Makuku da ta nan ne su ke bi ko dawowa in sun tafi satar mutane ko wani mugun aiki.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *