• Sun. Jan 16th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

SOJOJI BA ZA SU SHIGA LAMURAN ZABEN SUDAN A 2023-JANAR BURHAN

ByNoblen

Dec 6, 2021

Shugaban sojojin Sudan Janar Abdelfatah Burhan ya ce sojoji ba za su shiga lamuran zaben kasar ba da za a gudanar a a shekara ta 2023.
Burhan da ya amincewa da yarjejeniyar da ta dawo da gwamnatin mika mulki ta farar hula ta firaminista Abdallah Hamdok, ya ce sojoji za su bar madafun iko bayan zaben.
Burhan ya ce jami’an gwamnatin da a ka kawar da ma na gwamnatin Omar Elbashir ba za su shiga lamarin mika mulki hannun farar hula ba.
Game da murkushe masu zanga-zanga ta hanyar karfi har fiye da mutum 40 su ka mutu, Burhan ya ce sojoji sun kwantar da wadanda ke kawo tashin hankali ne a zanga-zangar.
Duk da amincewa da farar hula su ka yi na mika Elbashir ga kotun duniya, sojoji sun ki amincewa da nuna su na da fahimtar juna da kotun kuma za su dau mataki ne a lokacin da ya dace.
 

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *