• Sun. Jan 16th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

SIYASAR JARI HUJJA TA NAKKASA TATTALIN ARZIKI DA SANIN YA KAMATA A NAJERIYA-MASU SHARHI

ByNoblen

Dec 31, 2021 ,

Masu nazari kan lamuran yau da kullum a Najeriya da su ka hada da masana tarihi na aza alhakin koma bayan tattalin arziki da sanin ya kamata kan nasarar da ‘yan jari hujja su ka samu na amshe madafun iko da fakewa da cewa gyara su ke yi.
Duk da tsarin dimokradiyya a ke yi a Najeriya; masu sharhin sun ce ba a samun bambancin manufofin ‘yan siyasa a kowace jam’iyya don tsarin jari hujja da ke nesanta talakawa da masu hannu da shuni ya kulla dangantaka tsakanin su.
Masana siyasa na karfafa batun nan da ke cewa siyasa tamkar kasuwar bukata ce kowa na shiga don samun abun da ya ke muradi, don haka ba a samun makiyi ko masoyi na dindindin.
Bai zama abun mamaki ba a ‘yan kwanakin nan a ke ganin manyan ‘yan siyasa da a baya ba sa ga maciji da juna amma yanzu sun hade, duk da dama a bayan fage matan su kan yi hulda da juna inda su kan bar talakawa masu mara baya da wanzar da hamaiya ko ma kiyaiyar. 
A lokacin yakin neman zabe a kan samu matasa talakawa da ke marawa sassa biyu na ‘yan jari hujja; na arangama da juna alhali iyalan gwanayen su na can kuryar daki ko kasashen ketare su na karatu ko yawon shan iska.
Masanin tarihi Muhammad I Usman ya ce tuni ‘yan siyasa da dama sun sauka daga turbar da magabata su ka aza kasar tun 1960-1966.
Shi kuma Sheikh Hussein Zakariyya ya ce rashin samar da muhimman abubuwan more rayuwa, ya sa ‘yan jari hujja takaita ribar dimokradiyyar a gidajen su ko anguwannin su na GRA.
Musamman gwamnatin APC mai ci na cewa ta na tsayin dakan gyaran lamuran da su ka tabarbare ne a zamanin gwamnatocin baya da ba su yi fama da faduwar darajar fetur ko annobar korona bairos ba.
Gwamnan Yobe Mai Mala Buni shi ne shugaban riko na jam’iyyar APC.
Tun faduwa zaben PDP a 2015 da ya kawo hawa mulkin gamaiyar ‘yan adawa, Najeriya ta tsira daga mulkin jam’iyya daya, don haka ko banza dukkan sassa biyu sun dana mulki, wadanda su ka saura a bayan fage su ne ‘yan bama can ba ma nan.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
23 thoughts on “SIYASAR JARI HUJJA TA NAKKASA TATTALIN ARZIKI DA SANIN YA KAMATA A NAJERIYA-MASU SHARHI”
 1. Thanks for some other informative blog.
  Where else could I get that kind of info written in such
  a perfect means? I have a mission that I’m simply now operating on, and I
  have been on the look out for such info.

 2. What’s Happening i’m new to this, I stumbled upon this I’ve discovered It
  absolutely helpful and it has helped me out loads. I hope
  to give a contribution & help different customers like its helped me.
  Good job.

 3. I do believe all of the ideas you have introduced to
  your post. They are very convincing and will certainly work.
  Nonetheless, the posts are very short for novices.
  May you please extend them a little from next time?
  Thanks for the post.

 4. With havin so much content do you ever run into any issues of plagorism or copyright
  violation? My website has a lot of unique content I’ve either written myself or
  outsourced but it looks like a lot of it is popping
  it up all over the web without my authorization. Do you know any ways to
  help protect against content from being stolen? I’d truly appreciate it.

 5. Good day! This post couldn’t be written any better!
  Reading this post reminds me of my previous room
  mate! He always kept chatting about this.

  I will forward this write-up to him. Fairly certain he will have a good read.
  Many thanks for sharing!

 6. Greate post. Keep writing such kind of information on your page.
  Im really impressed by your site.
  Hi there, You have performed an incredible job.
  I will definitely digg it and in my opinion recommend to my friends.
  I am confident they will be benefited from this web site.

 7. I’m really inspired with your writing talents and also with the format in your weblog.

  Is this a paid subject or did you modify it yourself?
  Anyway keep up the nice quality writing, it is uncommon to peer a
  great weblog like this one today..

 8. Thank you for the auspicious writeup. It in reality used to
  be a amusement account it. Look advanced to far added agreeable
  from you! However, how could we keep in touch?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *