• Mon. Jul 4th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

SHUMO A KA KAMA BA BALERI BA-KOMRED WAZIRI

Masanin harkokin tsaro mazaunin Kaduna Komred Aliyu Waziri ya ce wanda jami’an tsaro su ka kama  a Kaduna ba mai satar mutane Baleri ba ne da wasu kafafe ke yadawa.

Waziri ya ce wanda a ka Kama sunan sa Abubakar Shumo da kan yi magana ko sharhi kan barayin daji a kafafen labaru.

Aliyu Waziri ya bukaci hukumomin da ke rike da Shumo su zurfafa bincike don gano gaskiya kar ya zama an ci zalin wanda bai aikata laifin da a ke tuhumar sa ba.

Masanin ya ce ya sha zama da Shumo a kafar labaru a Abuja inda su ka yi magana kan hanyoyin da za a shawo kan satar mutane.

Masanin ya ce Shumo ya taimaka wajen ceto rayukan mutane da dama daga hannun barayin daji.

Ko ma dai yaya, Komred Waziri ya ce alherin Shumo ya fi akasin sa yawa don ba ya shiga lamuran sata sai dai in hakan ta faru ya kan yi magana da barayin don kubutar da wadanda a ka sace.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “SHUMO A KA KAMA BA BALERI BA-KOMRED WAZIRI”
  1. Hey There. I found your blog using msn. This is an extremely well written article.

    I’ll make sure to bookmark it and come back to read more
    of your useful information. Thanks for the post.
    I will certainly comeback.

Leave a Reply

Your email address will not be published.