• Sat. May 21st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

SHUGABANNIN IGBO SU DAU MATAKI KAN YARAN SU – DATTAWAN AREWA

Majalisar dattawan arewa ta bukaci shugabannin ‘yan kabilar Igbo su ja kunnen matasan su ko ‘yan bindigar su da kan kashe da kona dukiyoyin ‘yan arewa.

Majalisar ta ce daukar matakin dakatar da ‘yan bindiga daga cigaba da zubar da jinin ‘yan arewa ne zai sa a kaucewa aukawa yaki.

Kungyar na cewa wannan yanayi na kashe-kashe shi ya haddasa yakin basasar Najeriya a 1967 inda dubban mutane su ka yi asarar ran su.

Dattawan na nuna tamkar shiru-shiru da hakurin ‘yan arewa ne ke sanya wasu na cin zarafin su a kudancin Najeriya.

Majalisar dattawan ta hada da su Farfesa Ango Abdullahi, Dr.Hakeem Baba Ahmed, Alhaji Tanko Yakasai da sauran su. Alhaji Sani Zangon Daura ya taba zama dan majalisar amma ya janye gabanin zaben 2019 don ya na marawa tazarcen shugaba Buhari da hakan ya saba da matsayin kungiyar na nuna shugaba Buhari bai cika alkawuran da ya dauka a ka mara ma sa baya tsawon shekaru har ya samu nasarar darewa karaga a 2015.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.