• Mon. Jan 17th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

SHUGABANNIN AFRURKA TA YAMMA SUN AMINCE DA BUDE KAN IYAKA

ByNoblen

Dec 14, 2021 ,

Shugaban kungiyar raya tattalin arziki ta kasashen Afurka ta yamma 15 ECOWAS sun amince da sake bude kan iyakokin su don samun damar hada-hadar jama’a a hukumance.
Za a bude kan iyakokin ne a ranar daya ga watan Janairun nan ta 2022.
An cimma matsayar a taron ministocin kasashen da a ka gudanar a Abuja ta hanyar taron manhajar yanar gizo.
Shugabannin sun yi la’akari da irin kalubalen tattalin arziki da rufe iyakokin ya yi kan tattalin arzikin yankin shi ya sa su ka dau matsayar bude iyakokin.
Jagororin na ECOWAS sun ce daga bariya zuwa bana, yankin ya yi asarar dala biliyan 50 sanadiyyar rufe kan iyaka.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “SHUGABANNIN AFRURKA TA YAMMA SUN AMINCE DA BUDE KAN IYAKA”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *