• Thu. May 19th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

SHUGABANCIN APC-SHUGABA YA MARA BAYA GA TAKARAR SANATA ABDULLAHI ADAMU

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya mara baya ga Sanata Abdullahi Adamu ya zama sabon shugaban jam’iyyar APC.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa shugaban ya baiyana mara bayan ne a taron da ya gudanar da gwamnonin jam’iyyar a fadar Aso Rock.
Majiyar ta fito ne daga gwamnoni masu ci da tsoffin gwamnoni ‘yan jam’iyyar mai gwamnatin taraiya.
Hakan ko bai zama umurni ba, amma babbar manunuya ce ta cewa Abdullahi Adamu wanda tsohon gwamnan jihar Nassarawa ne har sau biyu a tutar PDP, ya kama hanyar zama shugaban APC.
Kazalika labarin ya nuna za a tabbatar da Adamu a mtsayin sabon shugaban ne ba sai an yi takara da wasu ‘yan takarar ba.
Hakanan kwamitin riko na Mai Mala Buni ba ya aiwatar da wani aiki ba tare da sanin alkiblar shugaban ba, da dama shi ya rushe Adams Oshiomhole ya amince da kafa kwamitin rikwan.
Za a yi babban taron jam’iyyar APC a ranar 26 ga watan gobe.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
26 thoughts on “SHUGABANCIN APC-SHUGABA YA MARA BAYA GA TAKARAR SANATA ABDULLAHI ADAMU”
  1. I am really loving the theme/design of your web site. Do you ever run into any browser compatibility problems? A handful of my blog audience have complained about my website not working correctly in Explorer but looks great in Chrome. Do you have any solutions to help fix this problem?

Leave a Reply

Your email address will not be published.