• Mon. Jan 17th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

SHUGABAN TURKIYYA RACEB ERDOAN YA BADA AMINCEWAR A CIGABA DA NEMAN FETUR A GABASHIN MEDETIRENIYA

Shugaban Turkiyya Raceb Tayyeb Erdoan ya ba da amincewar jami’an sa, su cigaba da aikin neman mai a gabashin tekun medetireniya da a ka takaddama a kai.
Aikin neman man zai kai har watan yunin badi.

Jirgin ruwa na neman mai na Turkiyya “Oruc Reis” zai cigaba da aikin neman man a cikin tekun da kasar Cyprus da Girka ke cewa mallakar su ne.

Lamarin neman man a wannan yankin tekun na kara haddasa tankiya tsakanin Turkiyya da kungiyar taraiyar turai.

Erdoan ya yi barazanar kulle dubun dubatan ‘yan gudun hijirar Sham su shige turai, matukar kungiyar taraiyar turai ta cigaba da matsawa kasar sa lamba.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *