• Mon. Jan 17th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

SHUGABAN TSOHUWAR GWAMNATIN RIKWAN KWARYA TA NANJERIYA SHONEKAN YA RIGA MU GIDAN GASKIYA

Shugaban gwamnatin rikwan kwarya ta Najeriya a 1993 Chief Ernest Shonekan ya riga mu gidan gaskiya ya na mai shekaru 85 a duniya.
Shonekan ya mutu ne bayan fama da gajeruwar jinya a Lagos.
Marigayin ya zama shugaban gwamnatin rikwan kwarya ta Najeriya a fadar Aso Rock daga ranar 26 ga watan agusta zuwa 17 ga nuwambar 1993.
Shugaban mulkin soja Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya mika ragamar rikwan kwarya ga Shonekan inda daga bisa Janar Sani Abacha ya amshi ragamar.
A zamanin mulkin Shonekan an samu arahar shinkafa da kuma wani yadi da a ka rika sakawa mai rahusa da a ke yi wa taken Shonekan.
 

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “SHUGABAN TSOHUWAR GWAMNATIN RIKWAN KWARYA TA NANJERIYA SHONEKAN YA RIGA MU GIDAN GASKIYA”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *