• Sun. Jan 16th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

SHUGABAN NIJAR MUHAMMADOU ISSOUFOU YA YI TARON BANKWANA DA MAJALISAR SA

ByNoblen

Mar 29, 2021

Shugaban jamhuriyar Nijar mai barin gado Muhammadou Issoufoy ya yi taron bankwana da majalisar sa ta zartarwa don shirin mika mulki ga shugaba mai jiran gado Bazoum Muhammad a ranar biyu ga watan gobe.

A lokacin bankwanan, shugaban ya mika lambar yabo mafi girma ta kasar ga firaminista Biji Rafini.

Shugaba Issoufou ya yi nasarar mulki a wa’adi biyu na tsawon shekaru goma tun kawar da gwamnatin marigayi Muhammadou Tandja da amsar ragama da gwamnatin soja ta Salifou Jibo ta yi.

Dama ‘yan adawa karkashin dan takarar RDR Muhammad Ousmane sun yi watsi da sakamakon zaben da nuna an tabka magudi.

Jamhuriyar Nijar da ke yankin Sahel na cikin kasashen da ke fama da karancin tattalin arziki da hare-haren ‘yan ta’adda.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *