• Mon. Jan 17th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

SHUGABAN NAJERIYA MUHAMMADU YA ZIYARCI MAIDUGURI JIHAR BORNO

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ziyarci Maiduguri babban birnin jihar Borno inda ya kaddamar da wasu aiyuka da gwamnan jihar Babagana Umara Zulum ya aiwatar.
Shugaban wanda kafin ya iso ‘yan ta’adda sun tada wasu boma-bomai, ya cigaba da lamuran ziyarar sa da jawabi ga jami’an tsaro.
Shugaba Buhari ya ce a na gab da karya alkadarin ‘yan ta’addan ko a ce a na matakin karshe na murkushe su.
Kimanin fararen hula 5 su ka rasa ran su a sanadiyyar harin da ‘yan ta’addan su ka yi amfani da gurneti wajen kais hi a gewayen babban filin saukar jiragen sama na Maiduguri.
Boma-boman sun tashi sa’a daya gabanin saukar jirgin shugaba Buhari a filin jirgin na Maiduguri.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *